<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>339</hymn_number>
<title>Uba Na Sama, Allahnmu, Ka Dubi Ƙasarmu LW339</title>
<lyrics>[V1]
 1) Uba na Sama, Allahnmu, ka dubi ƙasarmu,
 Ka koya mana, ƴaƴanka, mu taya danginmu.

[V2]
 2) Ka sa mu bi tafarkinka, mu jawo kabilan nan,
 Su riƙa ba da gaskiya, su karƃi mulkinka.

[V3]
 3) Ya Allah, ba mu ikonka, mu tsare gaskiya,
 Mu kafa. shari'a daidai, mu hana rikici.

[V4]
 4) Ka koya mana dokoki, mu cika wa'adi,
 Mu zauna lafiya da duk jama'a ta ƙasarmu.

[V5]
 5) Nan gaba za mu yabonka domin ka cece mu.
 Kullum mu cika nufinka, mu yi ta aikinka.</lyrics>
</song>